✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za mu fara yi wa masu yi wa kasa hidima rigakafin COVID-19 – NYSC

“Za mu yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an samar da rigakafin cikin sauki.”

Shugaban Hukumar da ke Kula da Matasa Masu yi wa Kasa Hidima (NYSC), Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya ce daga yanzu za a fara yi wa matasan rigakafin COVID-19 daga sansanonin ba da horo.

Ya bayyana hakan ne ranar Talata a sansanin ba da horo na hukumar da ke Emure-Ekiti, a Karamar Hukumar Emure ta Jihar Ekiti.

Birgediya Janar Shuaibu, wanda ya yi magana ta bakin shugabar hukumar a Jihar, Misis Mary Chikezie, ya ce za a dauki matakin ne don ba su kariya daga cutar ta COVID-19.

Daga nan sai ya umarci matasan wadanda ba su kai ga karbar rigakafin ba, da su daure su yi hakan ba tare da bata lokaci ba.

“Ina son in tunatar da ku bukatar ci gaba da bin dokokin kariyar COVID-19 lokacin zamanku a sansanin ba da horo.

“Ku tabbatar kuna bayar da tzara, kuna amfani da takunkumi sannan kuma kuna wanke hannuwanku a kai a kai a wuraren da aka tanada.

“Kamar yadda kuka sani, Gwamnatin Tarayya ta sanar da tilasta nuna shaidar yin rigakafin cutar ga kowanne ma’aikacin gwamnati kafin ya sami damar shiga ofis daga ranar daya ga watan Disamba mai zuwa.

“Saboda haka, ina baku shawarar ku yi kokari ku ma ku yi kafin lokacin, saboda dokar har ku za ta shafa a wuraren ayyukan da za a tura ku.

“Za mu yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an samar muku da rigakafin cikin sauki kafin lokacin,” inji Shugaban na NYSC.

Kimanin matasa 1,451 ne aka rantsar a sansanin na Jihar Ekiti, wadda Alkalin Alkalan Jihar, Mai Shari’a Oyewole Adeyeye ya jagoranta, bisa wakilicin Mai Shari’a A. O. Familoni. (NAN)

%d bloggers like this: