✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Za a fara biyan Naira 77,000 ga masu yi wa ƙasa hidima daga Maris’

Babban Darakta Janar (DG) na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu yi wa…

Masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), za su fara jin daɗin sabon alawus ɗin gwamnatin tarayya na N77,000.00 wanda aka sake duba shi da za a fara biya daga watan Maris, 2025.

Babban Darakta Janar (DG) na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu yi wa ƙasa hidima a babban birnin tarayya, a ofishin NYSC na shiyya ta 3 da ke Wuse Zone 3 Old Parade Ground a yankin Garki a ranar Alhamis.

Ya sanar da masu yi wa  ƙasar hidima cewa ma’aikatar kuɗi ta sanar da Hukumar NYSC cewa an shirya kuɗaɗen alawus ɗin don fara biya.

Ya bayyana cewa jinkirin aiwatar da sabon alawus ɗin ya biyo bayan rattaba hannu ne kan kasafin kuɗi na shekarar 2025.

Yayin da yake yabawa mambobin NYSC bisa kiyaye manufofin shugabannin da suka kafa NYSC ta hanyar samar da haɗin kan ƙasa, haɗe kai da ci gaban ƙasa, shugaban NYSC ya roƙe su da su yi amfani da ma’anar yadda aka rubuta taken waƙen NYSC.