✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Za mu fafata ne da masu handame dukiyar kasa don kansu – Osinbajo

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya ce wadansu manyan ’yan siyasar kasar nan sun hadu waje daya sun hade baki domin yi wa Shugaba Buhari…

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya ce wadansu manyan ’yan siyasar kasar nan sun hadu waje daya sun hade baki domin yi wa Shugaba Buhari taron dangi a zaben 2019.

Farfesa Osinbajo ya fadi haka ne a yayin wani taro da wata kungiyar yakin neman zaben Buhari ta shirya, inda ya ce ’yan siyasar sun yi fatar mutuwar Shugaban Kasa a lokacin da ya yi fama da rashin lafiya.

Mataimakin Shugaban Kasar ya ce a zaben Febrairun 2019 da ke tafe, Buhari ne zai lashe zaben da gagarumar rinjaye.

“A zaben Febrairun 2019 da ke tafe, da yardar Allah APC za ta samu nasara. Za mu dawo da Shugaba Buhari a matsayin Shugaban Najeriya a karo na biyu. Zaben zai kafa wani sabon tarihi a kasar nan.

Kuma ku sani yaki ne za a yi tsakanin wadanda suke son sarrafa dukiyar kasar nan ta amfani kowa da kuma wadanda suke suke son azurta kansu kawai. Mutumin da ya tsaya haikan wajen yaki da batagari sannan yake muradin kyautata makomar ’ya’yanmu shi ne Muhammadu Buhari. Ba ina so in ce muku ya cika goma ba, amma dai mutum ne mai gaskiya da rikon amana,” inji shi..

Ya ce  “Sun yi gurin ya mutu amma bai mutu ba, maimakon haka ma sai ya dawo da cikakken lafiya da annuri bisa ikon Ubangiji, a wannan lokacin sun yi makoki a yayin da ’yan Najeriya suke murna da farin ciki. A sakamakon tsoron Buhari wadansu mutanen sun haukace. To amma yanzu kuma suna cewa wai wani daban mai suna Jubrin daga Sudan ne ba Buhari ba. A yayin da suka gaza kai shi kabari, sai suke da’awar bai wanzu ba.

“Amma fa suna nan a raye lokacin da Pastor Adeboye ya je har can Landan ya yi masa addu’a kwana guda kafin dawowarsa. Ta yaya wannan Jubrin din zai rika jagorantar zaman Majalisar Zartaswa ta Kasa, yana tattaunawa da ministoci sannan yana zantawa da ni a kullum? Dabararsu kwaya daya ce kawai: Idan ka yawaita yin karya, wadansu z asu gaskata ka….To Buhari ba wai yana raye kawai ba ne, da izinin Allah zai yi tsawon rai har bayan kammala wa’adinsa na biyu a duniya,” inji shi.