Wani saurayi da aka kama zai kai wa ’yan bindiga harsadai 837 da kuma rokoki hudu ya gurfana a gaban kotu a Jihar Kano.
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ce ta gurfanar da saurayin mai shekaru 19, wanda aka kama a a kan hanyarsa ta kai wa ’yan bindiga makaman Karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina daga Kano.
Matashin ya musanta zargin da ake masa, inda lauyansa, Murtala Isa, ya bukaci a ba da belinsa, rokon da lauya mai gabtar da kara, Hassana Habib Hassan ya kalubalanta.
Barisata Hassana ta ja hankalin kotun kan ba da belin ne bisa la’akari da cewa laifin ta’addanci da ake zargin matashin mai girma ne kuma zai iya tserewa idan aka ba da belinsa.
Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya amince ya ki ba da belin, sannan ya ba da umarnin sauraron shari’ar da wuri.
A cewarsa, duk da cewa doka ta amince a ba da belin wanda ake zargi, amma dole a yi hattara duba da girma da kuma sarkakiyan zargin ta’addanci da ake wa matashin, wanda ke da hadari ga al’umma.
Daga nan ya ba da umarnin tsare matashin a gidan yari, sannan ya dage zama shari’ar zuwa ranar 13 ga watan nan na Mayu.