✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za mu dage mulkin Najeriya ya koma hannun mutanen Kudu a Zaben 2023 —El-Rufai

Ba na shakkar Dattawan Arewa. Ni ma dattijo ne.

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, ya ce a matsayinsu na Gwamnonin Arewa za su yi iyakar kokari wajen ganin mulkin Najeriya, ya koma hannun mutanen Kudu a zabe mai zuwa.

Cikin wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, el-Rufai, ya ce “Duk wani zagon kasan da ake in sha Allahu zaben nan mun riga mun ci shi, kuma ba ja da baya za mu yi wannan yaki, za mu kuma kunyatasu mu nuna musu cewa mu ‘yan Arewa ba mutanen banza bane”.

Gwamnan na Kaduna ya ce, “Batun wani dattawa, ba wani dattawa, ni ma dattijo ne domin a wannan shekarar ta 2023 zan cika shekara 63, don haka su waye dattawan Arewa, mu gwamnonin Arewa mu ne dattawan Arewa kuma mu ne shugabannin Arewa.”

“Don haka mun ja layi sannan mun lashi takobin idan Allah Ya yarda za mu kunyata su,”  inji shi.

Cikin hirar tasa, El-Rufai, ya kalubalanci masu fakewa a bayan sabon tsarin canjin kudin Najeriya da manufar gurgunta dan takararsu na Shugaban Kasa a jam’iyyar APC.

Ya ce,“yawanci masu yin wannan abu ba ‘yan jam’iyya ba ne, mu muka yi jam’iyyar nan, mu muka yi yakin zabe, su kuma suka kwace gwamnati suke amfani da ita suna jin dadinta, sannan kuma suke yi wa jam’iyya zagon kasa suna yaudarar Shugaban Kasa.”

Gwamnan na Kaduna, ya ce idan ba zagon kasa ba, me ya sa za a ce sun shekara takwas suna gwamnati sai yanzu kusan zabe za a bullo da batun sauya takardun da kuma batun karancin mai da ake fama da shi a kasa?

Ya ce, “Kamar yadda ake yada wa a kafafan sada zumunta cewa muna zargin mataimakin shugaban kasa da zagon kasa, sam ba ruwan farfesa Osibanjo, wannan abu da ake munafunci ne na mutanen Arewa saboda suna so su munafunce mu da mu gwamnonin Arewa muka ce muna so Mulki ya koma kudu.”

Gwamnan na Kaduna ya ce “Sun jima suna irin wannan bita da kullin kallonsu kawai muke don lokaci ya kusa, amma a fito karara ana ba wa Shugaban Kasa shawarar da za ta kada jam’iyya, dole ne mu taka musu birki, kuma wallahi za mu yi.

“A yanzu duk gwamnonin APC gaba daya za mu je mu gana da shugaban kasa.”

Kazalika a cikin hirar, el-Rufai, ya ce jita-jitar da ake yadawa cewa wai suna wata tattaunawa karya ce, haka jita-jitar da ake yadawa wai shugaban kasa na ba wa dan takarar jam’iyyar adawa Atiku Abubakar, goyon baya karya ce, don kowa ya san shugaba Buhari ba zai taba yin wani abu da zai sabawa jam’iyyarsa ba.

El-Rufai, ya ce “Idan ka je ofishin shugaba Buhari za ku yi magan sosai, amma matsalar ita ce kana barin ofishinsa akwai wasu a ofis akwai kuma wasu a waje wadanda ba abin da suke so illa mu fadi zabe, sun kuma san kansu, kuma idan lokaci ya yi ko aka kai makura zan fadi ko su waye.”