✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu ci gaba da aikin haƙo ɗanyen mai a Arewa —NNPCL

NNPC ya sanar da shirinsa na kammala aikin shimfiɗa bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kano da kuma ci gaba da haƙo ɗanyen mai a…

Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya bayyana cewa zai ci gaba da aikin haƙa danyen mai a Arewa da ke yankin Kolmani.

Shugaban NNPCL, Bashir Bayo Ojulari ne ya sanar da aniyar kamfanin na ci gaba da aikin haƙar mai a yankunan arewa da gwamnatin Buhari da ta gabata ta fara.

Bayo Ojulari ya kuma addada aniyar NNPCL na kammala aikin bututun iskar gas da ya taso daga Ajaokuta a Jihar Kogi ya bi ta Abuja da Kaduna zuwa Kano (AKK).

A zantawarsa da kafar yaɗa labarai ta BBC, Injiniya Bayo ya ce, Za mu ci gaba da aikin haƙo mai a Kolmani da sauran wurare. Bayan aikin haƙo man, za mu kuma tabbatar da cewa mun gama aikin bututun man gas daga Ajaokuta zuwa Kano,” in ji shi.

A cewarsa, ayyukan haƙar man da na bututun iskar gas ɗin AKK za su taimaka wajen farfaɗo da kamfanonin da aka rufe a baya domin su ci gaba da aiki sannan a buɗe wasu sababbi.

“Wannan zai amfanar da yankin Arewa ta yadda kowa zai ci moriyarsa saboda za a samu bunƙasar arziki,” a cewarsa.

Game da ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan naɗa, inda ake zargin Shugaba Tinubu da fifita ’yan yankin Kudu wajen rabon mukamai a gwamnatinsa, shugaban na NNPC ya ce, shi ma ɗan Arewa ne, kuma ya yi maganganu a lokacin da aka sanar da naɗa shi.

Don haka ya buƙaci al’ummar Arewa da ma ƙasar baki ɗaya da su ba shi goyon baya, kuma su taimaka masa da addu’a domin ya samu nasarar ciyar da yankin da ma ƙasar gaba.