Rundunar sojojin Nijeriya a ranar Alhamis ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan kisan wasu mutane da ake zargin wasu sojoji sun yi a ƙauyen Sabon Birni da ke Ƙaramar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
Rundunar sojojin, wacce ta bayyana rahoton kisan a matsayin mai tayar da hankali, ta jajanta wa ‘yan uwan mutanen da lamarin ya shafa tare da yin alƙawarin gurfanar da duk wani jami’inta da aka samu da laifi da zarar an kammala binciken.
Aminiya ta ruwaito cewa mutanen ƙauyen suna zargin sojoji da kashe mutane uku da kuma shanu fiye da 100 a kasuwar shanu da yammacin Lahadi.
A hirarsu da Aminiya, wasu da lamarin ya faru a kan idonsu, sun yi iƙirarin cewa sojoji sun buɗe wuta kan shanun, lamarin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutane uku yayin da ‘yan kasuwar suka tsere domin tsira da ransu.
Sai dai da yake mayar da martani kan lamarin, kakakin rundunar sojin Nijeriya, Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike kan lamarin.
Manjo-Janar Nwachukwu, ya ce gudanar da bincike kan lamarin ya zama wajibi domin Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba wa rundunar sojin ƙasar damar kare rayuka da dukiyoyi, don haka ba za lamunci duk wani lamari da ke cin karo da hakan ba.
“Rundunar sojin Nijeriya ta kuma jajanta wa al’ummar Sabon Birni da iyalan waɗanda abin ya shafa.
“Muna jaddada cewa za a yi bincike sosai kan wannan zargi kuma duk wani jami’in da aka samu da laifi za a hukunta shi yadda ya kamata.
“Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ɗora wa rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, don haka ba za ta lamunci duk wani yunƙuri saɓanin hakan ba.”