✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu bayyana makarantu masu hana Kiristoci ibada —CAN

Nan gaba Hedikwatar CAN za ta bayyana matsayarta game da wannan tsari da nuna bambanci

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta yi barazanar bayyana manyan makarantun gwamnati da ke hana Kiristoci gina coci-coci yadda Musulmi ke gina masallatai.

Babban Sakataren CAN, Joseph Daramola, ya umarci shugabannin kungiyar na jihohi na shiyyoyin siyasa su mika sunayen makarantun gwamnati da ke nuna wa Kiristoci irin wannan wariya.

“Nan gaba Hedikwatar CAN za ta bayyana matsayarta game da wannan tsari da nuna bambanci,” inji wani bangare na wasikar da ya aike wa shugabannin kungiyar.

A cewarsa, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya umarci daukacin makarantun gwamnati da su bai wa Kiristoci wuraren da za su gina wadatattun coci-coci a a harabobinsu domin gudanar da ibada ba tare da tsangwama ba.

Amma ya ce duk da haka har yanzu hukumomin gudanarwar manyan makarantun na Gwamnatin Tarayya a wasu sassan Najeriya sun ki bin umarnin ministan.

A cewarsa, CAN na ba wa duk ’yan Najeriya tabbatacin yin aiki da masu ruwa da tsaki wajen ganin hukumomi na yi wa mabiya kowane addini adalci da ba su wuraren ibada.