Fulani makiyaya a Jihar Taraba sun yi sha alwashin bankadowa tare da kawar da masu aikata laifuka a tsakaninsu cikin wata biyar.
Sun yi wannan alkawarin ne a cikin wata sanarwar da suka fitar bayan wani taron makiyaya da shugabanninsu a kananan hukumomi 14 na jihar suka halarta a Fadar Sarkin Muri da ke Jalingo, babban birnin Jihar.
Taron ya kuma samu halartar mai bai wa gwamnan jihar, Darius Ishaku shawara kan harkokin tsaro.
Da yake karanta karanta takardar bayan taron, Shugaban Kungiyar Miyetti Allah, Reshen Jihar Taraba, Sahabi Tukur, ya ce Fulani makiyayan da shugabanninsu sun amince kada su rika boye masu laifi ko da kuwa ’ya’yansu ne ko ’yan uwansu.
Ya ce za a tantance tare da daukar bayanan wadanda suka taba daga cin masu laifin, wadanda suka ki taurin kai kuma tuba za a mika su ga jami’an tsaro.
Sahabi Tukur ya kara da cewa ko da yake aikin yana da wahala, amma ya zama dole don kare sunan Fulani makiyaya da dawo da martabarsu daga ayyukan laifi da bata-garin cikinsu ke aikatawa.
SAURAI: Yadda al’umma ke kare kansu daga ambaliya:
Shugaban makiyayan ya tabbatar wa sarkin cewa suna Fulanin jihar na goyon bayan duk wani mataki da zai iya kawar da bragurbi a tsakaninsu dari bisa dari.
A yayin wata ganawa da shugabannin Fulani a makon jiya ne Sarkin ya umarce su da su fallasa bata-garin cikinsu.
Da yake jawabi kan jajircewar makiyayan, sarkin ya ce umarnin nasa ya zama tilas ganin yadda ake samun karuwar satar mutane a yankin masarautar.
Ya ce a matsayinsa na shugaba mai kare gaskiya, ba zai taba lamuntar rashin adalci tsakanin talakawansa ba.
Sarkin ya koka kan yadda wasu gurbatattu daga cikin Fulani suka zubar kimarsu a Najeriya.
Ya gargadi mutane kan yi wa umarnin nasa mummunar fahimta, wanda a cewarsa, ya yi ne da nufin kyautata dabi’un Fulanin, wadanda dangi ne a gare shi.
Sarkin ya ce ya bayar da umarnin ne a matsayinsa na uba wajen daukar tsauraran matakai a kan ’ya’yansa lokacin da ya gano cewa suna aikata ba daidai ba.
Ya yaba wa shugabancin Fulanin kan daukar kwararan matakan kawar da masu laifin a cikinsu sannan ya ba da umarnin a mika masa jerin sunayen wadanda suka tuba da wadanda suka ki tuba.