✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu ɗauki masu gadi 400 a makarantun firamare — Abba

Za a ɗauki ma’aikatan ne daga kowacce ƙaramar hukuma domin su tsare sabbin azuzuwan da za a gina.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki ma’aikata 400 a kowace karamar hukuma da ke jihar domin gadin makarantun firamare.

Gwamnan ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce matakin wani ɓangare ne na ci gaba da aiwatar da ayyuka domin dawo da ƙimar ilimi a jihar.

Gwamnan ya ce “za a ɗauki ma’aikatan ne daga kowacce ƙaramar hukuma domin su tsare sabbin azuzuwan da za a gina da kuma tabbatar da lafiya da tsaron malamai da ɗalibai.”

Har wa yau, gwamnan cikin wata sanarwa ya bayyana ware kuɗi fiye da naira biliyan huɗu domin gina sabbin azuzuwa a makarantun firamare da ke ƙananan hukumomi guda 44 na jihar.