✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi zabe a Kasuwar Singa bayan hukuncin kotu – Alhaji Tijjani

kungiyar Jin Dadi da Walwalar ‘Yan kasuwar Kwanar Singa ta Jihar Kano ta musanta jita-jitar da ke yawo a gari cewa kungiyar za ta gudanar…

kungiyar Jin Dadi da Walwalar ‘Yan kasuwar Kwanar Singa ta Jihar Kano ta musanta jita-jitar da ke yawo a gari cewa kungiyar za ta gudanar da zabe a kwanan nan, inda kungiyar ta bayyana cewa za ta gudanar da zabe a duk lokacin da kotu ta yanke hukunci tsakanin kungiyar da kuma wata kungiyar da ke kasuwar Singar. 

Shugaban kungiyar na Riko Alhaji Tijjani Usman ne ya bayyana wa Aminiya hakan. Ya ce “kungiyarmu a shirye take ta gudanar da zaben sabbin shugabanninta da zarar kotu ta sallame su.b Kamar yadda aka sani mun tsara gudanar da zabenmu a wasu lokuta a baya, amma sai muka shiga kotu da wata kungiya da ke cikin wanann kasuwa, inda suke da’awar cewa wasu daga cikinmu ’ya’yan kungiyarsu ne,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa: “Don haka a cewarsu ba za mu gudanar da zabe ba. To mu kuma kasancewarmu masu biyayya ga kotu muka dakatar da wancan batu na zabe tare da zaman jiran umarnin kotu, don ita shari’a kamar mace ce da ciki ba a san me za ta haifa ba, haka kuma ba a san lokacin da za ta haihun ba,” inji shi.
Daga nan ya ce a shirye suke da zarar kotu ta sallame mu za mu gudanar da zabe kamar yadda muka shirya a baya.