A yau Litinin ne aka kaddanar da kwamitin shari’a da Gwamnan Jihar Kano ya kafa don binciken rikice-rikicen siyasa da mutane da suka bata.
Shugabar kwamitin, Mai Shari’a Zuwaira Yusuf ta bayyana cewa an dora wa kwamitin alhakin bincikar rikice-rikicen siyasa da kuma yawan batar mutane da ake yawan samu tare da bayar da shawarwari don magance matsalolin.
Ta kara da cewa kwamitin zai gano mutanen da aka jikkata a rikice-rikicen siyasa da wadanda jihar a manyan zabuban shekarun 2015 da 2019 da 2023 da kuma auna irin asarar da aka yi ta rayuka da dukiya.
Mai Shari’a Zuwaira ta bayyana cewa kwamitin zai lalubo hanyoyin taimaka wa mutanen da suka jikkata ta kowane bangare na tashe- tashen hankali a jihar.
- Hukuncin Rataya: Abduljabbar ya nemi a biya shi diyya
- An rufe makarantu saboda cutar kyanda a Adamawa
“Kwamitin zai bayar da shawarwari masu inganci don hana aukuwar rikice-rikicen siyasa a jihar a nan gaba,” in ji shugabar kwamitin.
Har ila yau a cewarta, kwamitin zai yi kokari wajen ganin cewa wadanda suka kitsa tashe- tashen hankula a zabukan 2015 da 2019 da 2023 sun fuskanci hukunci.
Ta kuma sha alwashin kwamitin zai gudanar da ayyukansa bisa gaskiya da adalci ba tare da tsoron, ko wata mummunar manufa ba.
“Ina son na sanar da jama’a cewa wannan kwamiui zai yi aikinsa bisa gaskiya ba tare da tsoro ba,
“Haka kuma muna gayyatar mutane ko kungiyoyi da wadanda aka jikkata a rikice rikicen da suka abku da ’yan uwansu ko ’yan uwan wadanda suka bace da su aika da bayanansu ko kuma korafinsu ga kwamitin daga wannan rana,” in ji ta.
Zuwaira ta yi kira ga ’yan jarida su ba kwamitin hadin kan da ya dace wajen nuna kwarewa a aikinsu na daukar rahoton ayyukan kwamitin.
Idan za a iya tunawa a watan Afrilu 2024 gwamnatin Kano ta kafa kwamitin shari’a don binciken rikice-rikicen siyasa da mutanen da suka bace daga shekarar 2015 zuwa 2023.