Masu mukamin Janar dain soja kimanin 30 ne za su yi ritaya bayan nada Manjo-Janar Faruk Yahaya a matasyin Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya.
Janar-Janar din da hakan za ta shafa su ne daliban Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soji (NDA) ’yan aji na 35 da aji na 36 kasancewar Manjo-Janar Faruk Yahaya dan aji na 37 —na baya da su ne.
Bisa al’adar soji, a duk lokacin da aka nada wani Janar a matsayin Babban Hafsan Soji, akan yi wa wadanda ke gaba da shi ritaya.
A ranar Alhamis, 27 ga Mayu, 2021, Shugaba Buhari ya nada Faruk Yahaya a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasa bayan rasuwar Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru wanda ke rike da mukamin.
Ranar Juma’a, 21 ga watan ne Attahiru da wasu Janar-Janar uku suka rasu a hatsarin jirgin sama tare wasu hafsoshi da jami’an soji a yayin ziyarar aiki a Kaduna, aka kuma yi jana’izarsu su 11 a ranar Asabar.
Hasashen nadi Babban Hafsan Soji
Nadin Faruk da Mukaddashin Daraktan Yada Labaran Hedikwatar Tsaro, Birgediya Onyema Nwachukwu ya sanar ta kawo karshen rade-radin wasu sunaye da ake cewa a cikinsu Buhari zai ba wa mukamin.
Da farko an yi hasashen za a nada Daraktan Tsara-tsare na Rundunar Sojin, Manjo-Janar Benjamin Ahanotu a matsayin sabon Babban Hafsan Sojin Kasan, kasancewarshi dan aji na 35 —ajinsu a marigayi Attahiru.
Bayan nada Faruk, majiyoyi a Rundunar sun ce hakan zai iya tilasta a yi wa Janar-Janar akalla 30 ’yan aji na 35 da 36 ritaya.
Akalla hafsoshi 28 ’yan aji na 35 ne suka rage a halin yanzu a Rundunar, ciki har da Manjo-Janar Sagir Yaro, wanda a kwanan aka nada shi Kwamandan NDA.
Majiyarmu ta soji ta ce karin girman da aka yi wa Faruk zuwa matasyin Manjo-Janar a 2017 ya sa ya sha gaban mutum takwas ’yan aji na 36.
‘Ana iya barin wasu’
An kuma gano cewa duk da cewa za a yi wa yawancin ’yan aji na 35 da 36 ritaya, Janar Faruk na iya rike wasu daga cikinsu, domin amfana da kwarewarsu musamman wajen yaki da Boko Haram a yankin Arewa-maso-Gabas.
“Aji na 34 sun riga sun tafi, marigayi Attahiru kuma dan aji na 35 ne. Akwai yiwuwar yi wa Janar-Janar 30 ritaya; biyu daga cikinsu ’yan aji na 35 ragowar 28 kuma ’yan aji na 36.
“Amma sabon Babban Hafsan Sojin Kasan na da damar barinsu. Zai so ’yan ajinsu su kasance a zagaye da shi. Saboda haka wasu za a sauya musu wurin aiki zuwa Hedikwatar Tsaro,” inji majiyar.
Wane ne Janar Faruk Yahaya?
A haifi Faruk Yahaya ne a ranar 5 ga Janairu, 1966 a garin Sifawa na Karamar Hukumar Bodinga ta Jihar Sakkwato.
A 1985 ya shiga Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soji (NDA) a matsayin dan aji na 37.
An yaye shi daga NDA a matsayin Laftanar a ranar 22 ga Satumba, 1990.
Ya yi karatun digirinsa na farko ne a fannin Tarihi, digiri na biyu kuma a kan Harkokin Siyasar Kasashen Duniya da Difilomasiyya.
Karin girma:
- Kwanan watan karin girman da ya samu kuma su ne:
- Laftanar – 27 ga Satumba, 1990
- Kyaftin – 27 ga Satumba, 1994
- Manjo – 27 ga Satumba, 1998
- Laftanar Kanar – 27 ga Satumba, 2003
- Kanar – 27 ga Satumba, 2008
- Birgediya – 27 ga Satumba, 2013
- Manjo-Janar – 27 ga Satumba, 2017.
Mukaman da ya rike:
A tsawon lokacin Faruk Yahaya ya rika mukamai daban-daban.
- Kafin sabon mukaminsa shi ne Kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai mai yaki da kungiyar Boko Haram; Ya kuma taba rike
- Babban Kwamandan Rundunar Sojin Kasa ta 1
- Kwamandan Rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram
- Kwamandan Rundunar Guards Brigade mai tsaron Fadar Shugaban Kasa
- Darekta a Kwalejin Hafsoshin Soji ta AFCSC da ke Jaji
- Darketa a Hedikwatar Rundunar Sojin Kasa
- Shugaban Ma’aikatan Rundunar Operation Pulo Shield da ta yaki ’yan taratsin Neja Delta
- Mataimakin Darektan Bincike da Cigaban Rundunar Sojin Kasa
- Sakataren Rundunar Soji Kasa
- Mataimakin Sakataren Rundunar Sojin Kasa
- Kwamandan Rundunar Operation Clean Sweep a yankin Birnin Gwari.
Manjo-Janar Faruk Attahiru ya kuma samu lambobin yabo masu yawa a lokuta daban-daban.