✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau za a yi jana’izar Janar Lagbaja

A Juma'ar nan za a gudanar da Jana'izar Soji ga tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja.

A Juma’ar nan za a gudanar da Jana’izar Soji ga tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja.

Jana’izar za ta gudana ne a Babbar Maƙabartar Soji ta Ƙasa da ke Abuja.

Janar Lagbaja ya rasu ne a bakin aiki a sakamakon doguwar jinyaa ƙasar waje.

A ranar Alhamis aka shigo da gawarsa Abuja inda aka gudanar da addu’o’i a Babban Cocin Barikin Sojoji na Mogadishu.

A yayin taron addu’o’in wanda manyan Hafsoshin Soji suma halarta, Kwamandan Kwalejin Horo kan Aikin Soji (TRADOC) Manjo-Janar Kelvin Aligbe, ya jinjina wa Lagbaja a matsayin jagora nagari.

Manjo-Janar Aligbe wanda ya gabatar da jawabi a madadin ɗaliban da ’yan Ajin 1992 da kayan kammala Makarantar Ƙanana Hafsan Sojoji ta NDA tare da Lagbaja, ya yi kira ga sojoji su yi koyi da kyawawan halayen Marigayin.