✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN zai kashe N50bn kan ma’aikatansa 1,000 da suka ajiye aiki

Mutum guda zai karɓi Naira miliyan 92 a matsayin kuɗin garatuti bayan aikin shekara huɗu a bankin CBN

Majiya mai tushe daga Hedikwatar Babban Bankin Nijeriya (CBN) ta bayyana cewa, bankin na shirin yi wa ma’aikatansa kusan 1,000 ritaya kafin lokacinsu a ƙarshen shekarar nan.

Wannan matakin zai ci sama da Naira biliyan 50 a matsayin haƙƙoƙin ma’aikatan da abin ya shafa.

Wata majiya a bankin ta bayyana cewa mutum daya zai samu kudin garatuti Naira miliyan 92, bayan aikin shekara huɗu a bankin.

Kwamitin Daraktocin CBN, ƙarƙashin jagorancin Olayemi Cardoso, ya dukufa wajen rage ma’aikata a wani bangare na sake fasalin tsarin.

A cikin watanni 10 da suka gabata, babban bankin na CBN ya sallami ma’aikata da dama, ciki har da daraktoci 17 na zamanin tsohon gwamna Godwin Emefiele, wadanda har yanzu ba a maye gurbinsu ba.

Wata takardar da CBN ta fitar, wadda wakikinmu ya gani, ta bayyana cewa ƙofar yin ritaya kafin lokaci (EPP) a buɗe take zuwa ranar 31 ga watan Disamban da muke ciki, ga dukkan matakan ma’aikata, zuwa ranar 7 ga watan Disamba.

Sai dai damar ba ta shafi ma’aikatan da har yanzu ba a tabbatar da su ba ko kuma ba su wuce shekara guda da fara aiki ba.

Wasu jami’ai sun bayyana cewa aƙalla ma’aikata 860 ne suka riga suka nemi takardar neman ajiye aiki. Shirin na son rai ne kuma yana ba da abubuwan ƙarfafawa don tashi da wuri, gami da fa’idodin kuɗi da waɗanda ba na kuɗi ba kamar shirin kuɗi da ƙarin kulawar likita.

Wani ma’aikaci ya bayyana cewa waɗanda ake sa ran ritayarsu suna matakin manajoji ne, musamman wadanda suka yi aiki lokacin tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele.

Majiyar ce, ma’aikacin da ya yi aikin shekaru huɗu zai karɓi Naira miliyan 92 zuwa Naira miliyan 97 matsayin kuɗin ritaya. Manaja na iya karbar Naira miliyan 64.5, inda kuɗin ke ƙaruwa gwargwadon shekarun aiki da matsayinsa da sauran shekarun da ya rage masa na aiki .

A yayin wani taro ta intanet Sashen Kuka da Ma’aikata na bankin ya jaddada manufarsa don cimma burin EPP, domin kauce wa ruɗani a tsakanin ma’aikatan.

Zuwa yanzu, ba a daraktoci 17 da aka kora watanni 10 da suka gabata, har yanzu, ba a maye gurbinsu ba, kuma a halin yanzu gurabunsu a CBN na ƙarƙashin jagorancin kodinetoci.

Wata takardar maye gurbin ta nuna cewa mataimakan daraktocin da ke kusa da ritaya ba su cancanci samun sabbin mukamai ba.

Bayan ƙorafe-ƙorafe nuna wariya, an buƙaci wasu mataimakan daraktoci da su nemi mukaman da babu masu rike da su.

A halin da ake ciki dai wasu korarrun daraktoci na neman kotu ta dawo da su domin hana maye gurbinsu, suna masu cewa korar da aka yi musu ya saba wa doka.

Da aka tuntube ta kan lamarin, Daraktar Sadarwa ta CBN, Hakama Sidi Ali, ba ta amsa ba.

Manufar na da nufin tabbatar da rarrabuwar kawuna tare da kayyade cewa yin ritaya na yau da kullum yana da shekaru 60 ko bayan shekaru 35 yana aikin.