✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi sanyi

Wani Bahadeje ne ya je wurin budurwarsa, suna cikin hira sai kawai hadari ya taso. Kafin ka ce me, an fara ruwan sama mai karfin…

Wani Bahadeje ne ya je wurin budurwarsa, suna cikin hira sai kawai hadari ya taso. Kafin ka ce me, an fara ruwan sama mai karfin gaske. Ganin haka sai baban yarinyar ya fito daga gida, ya ce mata: “Da alamu wannan ruwan ba mai tsagaitawa ba ne, watakila a kwana ana yi. Ki shiga ki gyara masa dakin baki, da safe sai ya tafi.” Nan da nan ta shiga gida ta fara gyara daki, tana gamawa sai suka fito ba su ga Bahadeje ba. Can sai ga shi nan ya shigo a guje, ya jike jagaf. Sai baban ya tambaye shi cewa: “Daga ina haka?” Sai saurayin ya ce: “Gidanmu na je na dauko bargona saboda na san za a yi sanyi cikin dare.”
Daga Nura Suleja, 09027377656