Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet), ta yi hasashen samun tsawa da mamakon ruwan sama a faɗin ƙasar nan daga ranar Laraba zuwa Juma’a.
Hasashen ya nuna cewa a ranar Laraba za a yi tsawa a sassan jihohin Jigawa, Kano, Katsina, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Taraba da kuma Adamawa.
Ana kuma sa ran za a samu cida a wasu yankunan jihohin Adamawa, Taraba, Jigawa, Kaduna, Yobe, Bauchi da kuma Gombe.
A yankin Arewa ta Tsakiya, babban birnin tarayya, Kwara, Kogi, Filato, Benuwe da Neja za su fuskanci tsawa da safe.
A ranar Alhamis ana sa ran za a yi tsawa a jihohin Filato, Nasarawa, Neja, Kogi, Kwara, babban birnin tarayya da kuma Jihar Benuwe.
A yankin Kudancin ƙasar nan, ana hasashen samun ruwan sama a jihohin Legas, Ondo, Delta, Ogun, Abiya, Ribas, Edo, Akwa Ibom, da Kuros Riba.
Har wa yau a ranar Alhamis ɗin, NiMet ta yi hasashen samun tsawa a sassan jihohin Kano, Katsina, Zamfara, Kaduna, Bauchi, Gombe, Adamawa, Borno, Yobe da Jigawa.
A yankin Arewa ta Tsakiya, za a samu tsawa da safe a babban birnin tarayya da jihohin Kwara, Kogi, da Neja, sai kuma cida a jihohin Nasarawa, Filato da Benuwe inda ake sa ran samun cidar da rana da kuma yamma.
Jihohin Kudancin ƙasar nan za su fuskanci ruwan sama da safe, inda ake sa ran samun ruwan saman zai kai har yamma.
A ranar Juma’a NiMet ta yi hasashen samun tsawa a jihohin Adamawa, Borno, Yobe, Bauchi da Gombe.
Yankin Arewa ta Tsakiya zai kasance cikin tsawa da rana, yayin da za samu hadari da yamma a babban birnin tarayya, Filato, Nasarawa, Neja, Benuwe, da Kogi.
Za a yi ruwan sama da safe a yankin kudu a jihohin Legas, Delta, Ribas, Bayelsa, Akwa Ibom, da Kuros Riba, inda za a ci gaba da yin samun ruwan saman har zuwa yamma.
NiMet ta buƙaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan da iska mai ƙarfi da kuma yiwuwar samun ambaliyar ruwa.
Kazalika, ta shawarci ma’aikatan jiragen sama da suke duba rahotannin yanayi domin zama cikin shiri da kuma kaucewa faɗawa cikin hatsari.