✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi Jana’izar Adamu Fika a Kaduna bayan La’asar

Fadar Sarkin Fika ta sanar da cewa a yau da La'asar za a yi jana'izar Adamu Fika a Babban Masallacin Sultan Bello da ke garin…

Fadar Sarkin Fika ta ayyana karfe 4 na yamma matsayin lokacin jana’izar Wazirin Fika, Malam Adamu Fika, wanda ya rasu yana da shekara 90 a duniya.

Sakataren Masarautar Fika, Ali Gimba Fika ya sanar da cewa a yau Laraba za a yi jana’izar a Babban Masallacin Sarkin Musulmi Muhammad Bello (Sultan Bello) da ke garin Kaduna.

Malam Adamu Fika Wazirin Fika shahararre ne kuma gogaggen malami kuma sanannen mai gudanarwa dan asalin garin Fika da ke jihar Yobe an haifeshi a shekarar 1933 a garin Fika dake jihar Yobe.

Adamu Fika shi ne Shugaban Ma’aikatan Najeriya na farko da ya yi murabus saboda bai ji dadin yadda wasu al’amura ke gudana ba a lokacin  da ya ke jagorancin ma’aikata, inda ya fahimci an gurbata ma’aikatan gwamnati.

An haifi Adamu Fika a shekarar 1933 inda ya yi makarantar firamare ta Fika daga 1941-45 da  Borno Middle School, Maiduguri a 1947.

Ya halarci Kwalejin Gwamnati a Kaduna (Kwalejin Barewa da ke Zariya a yanzu) daga 1948-51.

Daga nan ya zarce zuwa Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya 1952-1953 a lokacin tana matsayin Kwalejin Adabi da Kimiyya da Kere-kere ta Najeriya, a matsayin daya daga cikin dalibanta na farko.

Cibiyar Kididdiga da ke London a kasar Birtaniya a 1958 sai Cibiyar Nazarin Cigaba da ke Jami’ar Sussex, da ke Ingila, 1969; sannan Royal Institute of Public Administration, Jami’ar Manchester, UK, 1978.

Jerin Ayyuka da makaman da Adamu Fika ya yi

Malamin Lissafi da kimiyya a Kwalejin Barewa da ke Zariya – 1956.

Malami a Makarantar Sakandaren Gwamnati, Katsina-Ala, Jihar Benue – 1958.

Sufeton Ilimi na Lardi, Jami’in Ilimi na Lardi, Zariya – 1960.

Sufeton Ilimi, Lardin Adamawa, Yola – 1962.

Shugaban Kwalejin Horaswa ta Tarayya (FTC), Kaduna – 1962;

Mataimakin Sakatare, Hukumar Kula da Ayyukan Jama’a na Wucin Gadi, 1968-1970.

Kwamishinan Kudi, Jihar Arewa maso Gabas – 1972.

Babban Sakatare, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida  – 1975.

Babban Sakatare, Kwamitin Kasuwanci na Tarayya – 1979;

Babban Sakatare, Sashen Ayyukan Jama’a, Ofishin Shugaban Ma’aikata na Tarayya – 1981 – 1982.

Babban Sakatare, Sashen Harkokin ’Yan Sanda, Ofishin Zartarwa na Shugaban Kasa.

Babban Sakatare, Ma’aikatar Sadarwa, 1982-1984.

Babban Sakatare, Babban Birnin Tarayya kuma Shugaban Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya, Abuja, 1984.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, 1986.

Ya yi ritaya daga ma’aikatan gwamnatin tarayya, 1988;

Shugaban Hukumar Kwalejojin Ilimi ta Kasa, 1989-1990.

Sakataren Gudanarwa na Kasa da Gwamnatin Tarayya ta na nada na Jam’iyyar SDP, 1990.

Shugaban Hukumar Gudanarwa na Bankin UBA 1990-1993.

Magatakarda kuma Darakta-Janar na Majalisar Tarayya, 1992-1993.

Shugaban Farko, Hukumar Albashi ta Kasa  1992-1993.

Shugaban Farko, Hukumar Raba Dai-dai ta Kasa 1995-2001.

Shugaban Hukumar Gudanarwa na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) -2018