✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi fito-na-fito tsakanin PSG da Madrid a gasar Zakarun Turai

Za a buga wasan ne da Yammacin Talata a Parc de Princes a birnin Paris da ke Faransa.

A Talatar nan ce Paris Saint Germain da Real Madrid za su yi fito-na-fito a wasan farko na zagayen ’yan 16 a gasar cin Kofin Zakarun Turai na UEFA Champions League.

PSG na kokarin ganin ta kai ga matsayin lashe kofin gasar a karon farko yayin da Madrid take tunkaho da tarihin lashe kofin gasar har sau 13.

Madrid, wacce ta lashe kofin Super Copa a wannan shekara, ba ta kai ga wasan karshe a gasar ta UEFA ba tun bayan 2018.

Ana sa ran PSG za ta fito da zakukuran ’yan wasanta irinsu Lionel Messi, Kylian Mbappe, Angel Di Maria da Sergio Ramos da Neymar a wasan, wanda za a yi a zagayen na farko.

A bangaren Madrid, masu bibiyar kwallon kafa sun zuba ido su ga ko dan wasanta Karim Benzema wanda ya farfado daga jinya zai buga wasan.

Kwana 21 ya kwashe ba ya kwallo, hakan ya sa bai samu damar buga wasannin uku ba na bayan nan da kungiyar ta buga.

Masu ruwa da tsaki a fannin tamaula sun yi hasashen cewa, Mauricio Pochettino zai buga wasan a tsarin 4 baya, 3 tsakiya da kuma 3 gaba wato 4-3-3 ke nan, inda Gianluigi Donnarumma zai tsare raga, Achraf Hakimi, Marquinhos, Presnel Kimpembe da kuma Nuno Mendes a baya.

Leandro Paredes ne zai ja ragamar yan wasan tsakiya da kungiyar ta PSG ake hasashen za ta fito da su a wasan, inda Marco Verratti da Georginio Wijnaldum za su taimaka masa, yayin da kuma yan gaban ake sa ran za su kunshi Lionel Messi, Kylian Mbappe da kuma Neymar.

Shi ma Carlo Ancelotti ana sa ran zai fito da ’yan wasansa a tsarin makamancin na PSG wato 4-3-3, inda za a fito da Thibaut Courtois a matsayin mai tsaron raga, sannan kuma a fara da Dani Carvajal, Eder Militao, David Alaba da Ferland Mendy a matsayin ’yan wasan baya.

Casemiro da Luka Modric da kuma Toni Kroos za su rike tsakiya, yayin da Karim Benzema zai jagoranci ’yan gaba kuma ana sa ran Marco Asensio da Vinicius Junior ne za su taimaka masa a gefe da gefe.

Za a buga wasan ne da Yammacin Talata a Parc de Princes a birnin Paris da ke Faransa.

A gefe guda kuma, Sporting CP ta kasar Portugal ce za ta karbi bakuncin Manchester City a nasu wasan na zagayen ’yan 16