Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet), ta sanar da karewar yanayin damina a Arewacin kasar nan, inda ta ce wasu sassan yankin za su fuskanci yanayin kura da hazo nan da kwanaki masu zuwa.
NiMet a hasashenta ta ce kura za ta taso daga jamhuriyar Nijar kuma za ta mamaye sassan Arewacin na Najeriya.
- Mutum 2 sun gurfana a gaban kotu kan zargin bata sunan Ganduje a wasan barkwanci
- Kyankyaso: Kwaron da ke iya rayuwa tsawon mako daya babu kai
Guguwar iska mai karfin mita 800, a cewar NiMet, za ta kai kurar zuwa Arewacin kasar nan da kuma Arewa ta Tsakiya.
Binciken ya kuma nuna cewa ana sa ran za a samu karin kura da hazo a yankin.
“A cikin sa’o’i 24 masu zuwa, akwai yiwuwar karin hazo da kura (a matsakaicin nisan zango mita 2000 – mita 5000) a jihohin Borno, Yobe, Katsina, Kano, Kaduna, Gombe, Bauchi da Jigawa, yayin da sauran jihohin Arewa (ciki har da Arewa ta Tsakiya) na iya fuskantar yanayin zafi kan mataki 5-7.
“Ana sa ran wannan yanayin zai ci gaba har zuwa kwanaki uku masu zuwa.”
NiMet ta kuma ce yawan zafin rana zai karu a hankali.
Hukumar ta shawarci masu ababen hawa da su rika yin tuki cikin natsuwa a wannan yanayi.
“Hakanan mutanen da ke da matsalar numfashi ya kamata su yi taka tsantsan, musamman a lokutan da suke waje,” inji NiMet.
Ta kuma shawarci ma’aikatan jirgin sama da su nemi sabbin rahotannin yanayi daga ofisoshinta don inganta ayyukansu.