Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce tana gab da yin dokar ba wa kananan yara kariya a jihar.
Kwamishinan harkokin mata, Kulu Abdullahi Sifawa ta ba da tabbacin yin dokar a taron bikin zagayowar Ranar ‘Ya’ya Mata ta Duniya.
“Dokar za ta kare yaranmu kanana musamman mata daga nau’ikan cin zarafi domin za ta hukunta dukkannin nau’ukan cin zarafinsu”, inji ta a lokacin da take cewa kudurin na matakin karshe na zama doka.
Kwamishinar ta bakin Daraktar bunkasa rayuwar mata da yara, Kulu Nuhu, ta ce ma’aikatar ta kafa cibiyar wayar da kan iyaye da kuma taimaka wa wadanda aka ci zarafi a jihar.
- An soke biyan kudin makaranta a Abuja
- Za a rataye mai yaudarar mata yana kashe su
- Masu garkuwa da mutane shida sun shiga hannu
Tun da farko, jami’ar Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a jihar, Safiya Tahir ta ce amfanin ranar kare yaran shi ne tallata ‘yancin mata da yara.
Ta ce taron kara wa juna sani da za a yi zai tattauna abubuwan da suka shafi samar ilimin yara, cin zarafi da kuma tallafawa.
A jawabinsa, Shugaban Huumar Ilimin Bai-daya ta Jihar, Shu’iabu Gwanda Gobir ta bakin Darektan kula da Ilimin a Matakin Farko, Ibrahim Aliyu, ya ce har yanzu ilimin samar da ilimi ‘ya’ya mata na fuskantar babbar matsala a Jihar.
Taron ya samu halarcin dalibai mata daga jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da kuma masu fafutikar kare hakkin mata da sauransu.