Kungiyar Cigaban Jihar Sakkwato (SOSDA), ta bukaci hukumar jarabawar NECO ta yi mata bayanin dalilin hukumar na kin sakin sakamakon jarabawar daliban jihar na 2019.
Wakilin Aminiya a Sakkwato, ya rawaito cewa, NECO ta ki sakin sakamakon jarabawar daliban ne saboda rashin warware wasu matsaloli tsakaninta da gwamnatin jihar.
Gwamnatin jihar kan biya wa daliban ajin karshe na sakandare da ke makarantun gwamnati kudin jarabawar NECO ta kammala makarantun.
- El-Hamzat ya zama Daraktan Gudanarwan asibitin UDUTH
- An karrama direban Sardauna a bikin shekara 50 da kafa Gidan Arewa
- KEDCO ya fara raba mitocin wutar lantarki kyauta a Kano
A takardar da SOSDA ta aike wa NECO, shugabanta da magatakardanta, Malami Mohammed Galadanci da Abubakar Alkali, kungiyar ta ce cigaban dalibi yana samuwa ne ta hanyar ciyar da shi gaba a karshen kowace shekarar karatu.
“Muna son jin dalilan da za su gamsar da mu daga bakin NECO, abin da ya sa har yanzu ba a saki sakamakon jarabawar ba alhali tuntuni an saki na ’yan uwansu na wasu jihohin da suka zauna jarabawa tare da su a shekarar karatu ta 2019/2020”, inji SOSDA.
Kungiyar ta yi kira da masu ruwa da tsaki a jihar su saka baki a saki sakamakon jarabawar dalibai ’yan asalin Jihar Sakkwato.
Ta ta kuma kirayi gwamnatin jihar da ta dauki dukkan matakin da ya dace don ganin an saki sakamakon daliban.
SOSDA ta ce, tana da tabbacin cewa NECO a shirye take ta taimaka da duk abun da za ta iya taimakawa da shi na ganin an saki sakamakon jarabawar daliban jihar don su samu damar dorawa da ci gaba da karatunsu.