’Yan sanda sun kama wata mata bisa zargin azabtar da dan rikonta mai shekara shida a Unguwar Kwado, cikin birnin Katsina.
Matar ma’aikaciya ce a ofishin Hukumar Samar da Ayyukan ta Kasa (NDE) da ke Katsina, kamar yadda bincike ya nuna.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, Gambo Isa, ya ce an kama matar ce a ranar 15 ga watan Satumba bisa zargin cin zarafi da azabtar da yaron.
Ya ce a a yayin bincike an gano raunuka a sassan jikin yaron da kuma karaya a kafarsa ta dama.
Isa ya ce ana kan binciken lamarin kuma an kai yaron Babban Asibitin Katsina inda ake yi masa magani.
Da take amsa tambaya, wadda ake zargin ta ce mahaifin yaron ne ya kawo mata shi riko bayan rabuwarsu da uwar dan, kuma ba ta san shi ba sai a lokacin.
Ta ce ko kafin a kai mata yaron akwai raunuka a jikinsa saboda yana yawan dauko magana da bugun ’ya’yan makwabta da kartar fentin mutane, wanda hakan ya sa masu riko da dama suka rabu da shi.
Sai dai wata majiya ta ce ko a baya ’yan sanda sun taba kama ta bisa zargin daure wa yaron hannu da kafafu ta kuma tsare shi a cikin gidanta.
Majiyar ta ce a wancan lokacin matar ta yi karyar cewa ta dauko rainon yaron ne daga Kano bayan iyayensa sun mutu a hatsarin mota.
Ta ce, ta yi karyar ce saboda wasu mutane na kokarin kai shi gidan rainon yara, kuma mahaifinsa baya kula da shi.
A bayaninta, mahaifiyar yaron ta ce ubansa ya karbe shi daga hannunta ne da cewar za a yi masa kaciya amma ya ki mayar mata da shi ba.
Shi kuma mahaifin yaron ya ce abokinsa ne ya hada shi da matar kuma a duk lokacin da ya ce zai zo duba shi sai ta ce ta yi tafiya.