Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode ya bukaci mawallafiya a intanet, Dimokorkus, ta biya shi diyyar Naira biliyan biyu saboda zargin bata masa suna a shafinta.
Ya ce rahoton ta Stella ta wallafa na zargin cewa matarsa Precious Chikwendu ta rabu da shi ne saboda cin zarafinta, kuma tsohon ministan ya kwace ’ya’yan da suka haifa, tare da umartar ta kada ta sake kusantar gidansa.
- Za a bude makarantu ranar Litinin a Taraba
- Matattun ma’aikata 333 ne ake karbar albashi da sunansu a Jihar Neja
- Mahara sun kashe mutum sun sace 17 ’yan gida daya
“Mun ba ki wa’adin kwana 14 daga ranar da kika samu wannan wasika ki yi abubuwan da muka zayyana, ko kuma wanda muke wakilta ya je kotu domin neman mafita”, inji wasikar da lauyoyinsa suka aike wa marubuciyar.
Wasikar daga Ahmed Raji & Co. ta bukaci Stella ta da ta ba tsohon ministan hakuri a manyan jaridu guda biyu sannan ta biya shi diyyar Naira biliyan biyu.
“Wanda muke bukata ya ji zafi ya kuma nemi mu ja hankalinku game da bata masa suna da na iyalansa. Sakamakon rubutun wanda muke wakilta ya samu kiraye-kiraye da sakonni marasa dadi daga sassan duniya da ke nuna kimarsa ta zube.
“Duk da haka a shirye yake ya kau da kai idan har kika janye zargin a dandamlin da kikda wallafa sannan ki ba shi hakuri a cikin manyan jaridun kasa guda biyu.
“Muna neman ki da ki fara tattaunawa da mu kan biyan diyyar biliyan N2 da bai taka kara ya karya ba”, inji wasikar.
Shekaru biyar da suka gabata ne Fani-Kayode da Precious wadda tsohuwar sarauniyar kyau ce suka yi aure.
Sun haki ’ya’ya hudu maza cikinsu har da ’yan uku da ka haifa a 2018.