Jam’iyyar adawa ta PDP, ta yi Allah-wadai da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bayan ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan cin zarafinta.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran PDP na Ƙasa, Debo Ologunagba, ya fitar, jam’iyyar ta ce dakatarwar wata hanya ce ta ɓoye zargin da ake yi wa Akpabio.
- Kisan malami: Shugabannin Kiristocin Kudancin Kaduna sun yi Allah-wadai
- Najeriya ta kama hanyar gyaruwa – Remi Tinubu
“Wannan mataki ba wai kawai ya hana Sanata Akpoti-Uduaghan damar kare kanta ba ne, har ma yana nuna cewa majalisar na kare rashin ɗa’a,” in ji PDP.
Jam’iyyar ta kuma ce dakatarwar ba adalci ba ce ga al’ummar yankin Kogi ta Tsakiya, waɗanda yanzu suka rasa wakilci a majalisa.
“Wannan cin zarafi ne da amfani da muƙami ba daidai ba, domin Akpabio na ci gaba da zama a kujerarsa duk da irin wannan zargi mai girma.
“Idan har bai da abin ɓoyewa, ya sauka don bayar da damar gudanar da bincike na gaskiya,” in ji PDP.
PDP ta nuna cewa ba wannan ne karon farko da ake zargin Akpabio da aikata irin wannan ba.
Ta ce tsohuwar Shugabar Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Dokta Joi Nunieh, ta taɓa yin irin wannan ƙorafi a kansa.
Jam’iyyar ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa da ya kare sunansa ta hanyar amincewa da bincike maimakon ƙoƙarin ɓoye gaskiya.