✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha

Natasha ta ce za ta ci gaba da yi wa al'ummarta aiki duk da dakatarwar da aka yi mata.

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta bayyana dakatar da ita da Majalisar Dattawa ta yi, a matsayin rashin adalci.

An dakatar da ita ne biyo bayan ta ƙaddamar da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan tsarin zama a zauren majalisa a ranar 20 ga watan Fabrairu.

Daga baya, ta zargi Akpabio da cin zarafinta, amma ya musanta hakan.

Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na majalisar, ya yi watsi da koken nata, inda ya bayyana cewa ba a bi ƙa’ida wajen shigar da ƙorafin ba.

Duk da haka, Natasha ta jaddada cewar ita Sanata ce, kuma za ta ci gaba da wakiltar al’ummarta.

A cikin wani rubutu da ta wallafa a shafukan sada zumunta, ta ce: “Dakatar da ni ba bisa ƙa’ida ba ya saɓa wa adalci da gaskiya.

“Ba zai karɓe min matsayin da ’yan Kogi suka ba ni ba. Zan ci gaba da yi wa mutanena da ƙasata hidima har zuwa 2027—da ma bayan hakan.”

Majalisar ta dakatar da ita na tsawon watanni shida bayan karɓar shawarar kwamitin Ladabtarwa.

Matakin dai ya haifar da zazzafar muhawara s tsakanin ‘yan Najeriya, inda wasu ke ganin an tauye mata haƙƙinta.