Ministar Harkokin Mata, Imaan Suleiman Ibrahim, ta yi alƙawarin sasanta Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Majalisar Dattawa ta dakatar da Natasha, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya, na tsawon watanni shida bayan kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a ya same ta da laifin karya dokokin majalisar.
- Fashewar tankar mai: Mutum 7 sun mutu, gonaki sun lalace a Neja
- Majalisar wakilai na shirin ƙwace rajistar jam’iyyu daga hannun INEC
Yayin da ta ke magana da manema labarai bayan taron bikin Ranar Mata ta Duniya, ministar ta bayyana takaicinta kan dakatarwar da aka yi wa Natasha.
Ta ce, “Abin takaici ne kuma bai kamata ya faru ba. A majalisa ta baya, muna da mata Sanatoci guda tara, amma yanzu huɗu ne kawai suka rage.
“Ba ma son rasa kowace mace a majalisa, sai dai mu ƙara yawansu.”
Ta kuma tabbatar da cewa ana ƙoƙarin shawo kan lamarin.
“Za mu tabbatar da cewar an samu zaman lafiya ta hanyar tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki, tare da tabbatar da cewa an yi adalci.
“Shugaban Majalisar Dattawa da kansa ya ce a shirye suke domin a sasanta. Za mu zama masu shiga tsakani don haɗa kan ɓangarorin biyu da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin maza da mata a shugabanci,” in ji ta.
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan yadda mutane daban-daban ke tofa albarkacin bakinsu kan taƙaddamar da ta ɓarke tsakanin Natasha da Akpabio.