Firaministan Pakistan Imran Khan zai fuskanci matakin tsigewa bayan da Kotun Koli ta ce rusa Majalisar Dokoki da firaminista ya yi haramtacce ne kuma lallai ne majalisar ta ci gaba da kada kuri’ar rashin amanna da hakan.
Kotun kolin Pakistan ta yanke hukuncin cewa matakin da Firaminista Imran Khan ya dauka na rusa majalisar dokoki haramtacce ne ta kuma ba da umarnin majalisar ta ci gaba da shirinta na kada kuri’ar rashin amanna da matakin.
- Najeriya ce ta 3 a kasashen da suka fi cin naman kare a duniya —Bincike
- Ya zama wajibi Jamus ta ba wa Ukraine makamai —Scholz
Kotun dai ta yi umarni majalisar ta dawo a ranar 9 ga watan Afrilu domin ci gaba da kuri’ar rashin amannar.
’Yan adawa sun ce suna da kuri’u 172 da ake bukata daga cikin kujerun Majalisar Dokokin 340 domin tsige Firaministan.
A bayan nan ne Imran Khan ya rusa Majalisar Dokokin Pakistan, matakin da ke nufin wajibi ne a gudanar da zaben ’yan majalisar dokoki a cikin kwanaki 60, sabanin shekara mai zuwa da aka tsara gudanar da zaben tun da farko.
Alkaluma sun nuna cewa Pakistan dai tana da tarihin rikicin shugabanci kala-kala.
Tun daga shekara 1947, lokacin da kasar ta samu ’yancin kai daga Turawan Birtaniya, babu firaministan da ya taba yin cikakken wa’adin shekaru biyar ba tare da an yi masa juyin mulki ko kuma rikicin siyasa ya kawar da shi ba.
A shekara ta 2018 ne dai Firaminista Khan mai ci ya hau mukamin.