✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a toshe layukan waya marasa Lambar Dan Kasa cikin sati biyu

Duk layin SIM da ba a yi wa rajista da lambar NIN ba to za a toshe cikin sati biyu

Gwamnatin Najeriya ta ba kamfanonin sadarwa a kasar sati biyu su rufe layukan wayan da masu su ba su yi musu rajista da lambar Shaidar Dan Kasa (NIN) ba.

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ce ta ba da umarnin a zamanta da kamfanonin sadarwa kan umarnin rufe rajistar sabbin layukan waya da Najeriya.

“Za a fara karbar lambar NIN na masu amfani da waya daga yau 16 ga wata, a rufe rufe a ranar 30 ga watan Disamba, 2020; daga ranar za a toshe layukan SIM marasa lambar NIN”, inji NCC.

Kakakin Hukumar, Ikechukwu Adinde, ya ce Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isah Ali Pantami ya yi zaman da kamfanonin da kuma hukumomin da ke karkashin ma’aikatarsa ne don ganowa da kuma dorawa a kan nasarorin da aka samu a wurin aiwar da umarninsa na farko.

“Masu ruwa da tsakin sun yi ittifaki cewa wajibu a hanzarta a kuma inganta tsarin yin rajista layukan waya ba tare da rufa-rufa ba”, inji shi.

Matakin na da alaka da kokarin dakile matsalolin ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran manyan laifukan da ke addabar Najeriya wadda ko a ranar Juma’a sai da ’yan bindiga suka yi garkuwa da daruruwan dalibai a makantar GSSS Kankara, Jihar Katsina.

Lamarin ya sa aka rufe makarantun kwana a fadin jihar yayin da makwabciyarta, Jihar Zamfara ta rufe makarantu a yankunan da ke iyaka da Jihar Katsinar da ma Jihar Kaduna, wadanda kowannensu ke fama da matsalar tsaro.

Ana kyautata zato cewa samun cikakken bayan masu amfani da layukan waya zai bada cikakkiyar damar bibiya da kuma damko masu aikata laifukan a kasar.

 

Dokar NCC ga kamfanonin sandarwa:

Sauran umarnin da kamfanonin sadarwan za su aiwatar su ne:

Ci gaba da bin umarnin hana yin rajistar sabbin layukan waya.

Duk masu layukan waya su gabatar da lambarsu ta NIN a kara a kan rajistar da suka yi a baya.

Za a fara daga ranar  16 zuwa30 ga watan Disamba 2020.

Ranar 30-12-2020 za a toshe duk layin waya mara lambar NIN.

Za hukunta kamfanonin da ya saba da za ta iya kaiwa ga kwace lasisi.

Kwamitin da ya kunshi Minista, shugabannin kamfanonin sadarwa da sauran masu ruwa da tsaki za su sa ido kan biyayya ga umarnin.