Kwamitin Shugaban Kasa kan yi wa tubabbun tsagerun Neja Delta afuwa ya yi kira gare su da su tsara sabbin dabarun kasuwanci don a taimaka musu su zama masu dogaro da kansu.
Shugaban riko na kwamitin, Kanal Milland Dixon Dikio (mai ritaya) ne ya yi kiran lokacin da yake jawabi ga rukunin farko na wadanda shirin ya shafa da aka zabo daga jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba a karshen mako.
- Mahara sun kashe mutum daya, sun kona gidaje da motoci a Zangon Kataf
- Kishi ya sa wata mata cinna wa kanta wuta a Jigawa
Kakakin shugaban, Mista Nneotaobase Egbe ya fada a cikin wata sanarwa ranar Asabar cewa manufar shirin ita ce ba wai kawai su ci gaba da dogaro da N65,000 din da ake basu a kowanne wata ba ne, sai don su zama suna daukar nauyin wasu.
Dikio ya ce, “Ina so in karfafa muku gwiwa ku rubuto tsare-tsaren kasuwancinku don mu taimaka muku ku dogara da kanku. Za mu shirya muku bitocin kasuwanci don koya muku ingantattun hanyoyin samu kudi kuma na halal.
“Mu a karkashin ofishinmu ba ma bayar da kwangiloli, kawai muna bayar da horo ne da tarbiyya ga tubabbun tsageru. Wannan ita ce sabuwar manufarmu a yanzu.
“Babban burinmu a wanannan shirin shi ne daga karshe kowa daga cikinmu zai sami fa’ida.
“Akwai damammaki iri-iri ba wai kawai biyan kudi ba. A matsayinmu na wadanda abin ya shafa, ya kamata mu yi amfani da su wajen bunkasa yankinmu.
“Alal misali, za mu iya rungumar harkar sufurin jiragen ruwa hannu bibbiyu,” inji sanarwar.