✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci

Da zarar an ce watan Ramadana ya kama wasu daga cikin harkokin kasuwancin kan samu naƙasu.

More Podcasts

Hausawa sun yi gaskiya da suka ce ‘yawan mutane su ne kasuwa’.

Yawan hada hadar da ake yi tsakanin ‘yan kasuwa da abokan cinikinsu na ɗaya daga cikin abun da zai tabbatar maka kasuwanci na gudana kamar yadda ake so.

Sai dai da zarar an ce watan Ramadana ya kama wasu daga cikin harkokin kasuwancin kan samu naƙasu, yayin da wasu kuma ke haɓaka.

Wasu kuwa kasuwar ce ke sauya salo, inda take dakushewa a wasu sa’anni ta kuma haɓaka a wasu sa’anni.

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan yadda wasu harkokin kasuwancin ke haɓaka da kuma yadda wasu ke samun koma baya cikin watan Azumin Ramadana.

Domin sauke shirin, latsa nan