Hukumar shirya zabe ta Jamhuniyar Nijar (CENI), ta sanar da cewa za a tafi zagaye na biyu kafin sanar da zababben shugaban kasar.
Wannan hukunci ya zama tilas a cewar hukumar, inda ta ce daga cikin ’yan takarar babu wanda ya samu kaso 50.1% daga kuri’un da aka kada.
- Yadda na haihu a hannun ’yan bindiga —Mai jego
- Wata mata ta antaya wa kishiyarta tafasasshen ruwa
- Nijar: Mutum miliyan 7.4 na zaben Shugaban Kasa
- Dahiru Mangal ya ba dan takarar Shugaban Kasa a Nijar gudunmuwar motoci 100
Kashin farko na zaben an gudanar da shi ne ranar 27 ga Disamba 2020, inda ’yan takara 30 suka fatata, ciki har da dan takarar jam’iyya mai mulki kuma toshon minista, Mohammed Bazoum.
CENI, ta ce Bazoum ya samu kaso 39.33% cikin dari, da kuma kuri’u 1,879,000.
Shi kuma Mohammed Ousmane, na jam’iyyar RDR Canji, ya samu kaso 16.99% cikin dari, wato kuri’a 811,838.
An tsayar da ranar 21 ga watan Fabrairun 2021, a matsayin ranar da za a shiga zagaye na biyu na zaben Shugaban Kasar.