Babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ta musanta rahotannin da ke cewa tana zawarcin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, domin yi mata takarar shugaban ƙasa a 2027.
Mai magana da yawun jam’iyyar PDP na ƙasa, Ibrahim Abdullahi, ya ce wannan rahoto ba gaskiya ba ne.
- Gobara: Gwamnatin Yobe ta tallafa wa ’yan kasuwar Damaturu da Gashua
- Zamana a gidan yari jarabawa ce daga Allah – Farouk Lawan
A cewarsa: “Babu wani lokaci da PDP ta miƙa wa Jonathan tayin takara ko ta buƙace shi ya fito takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.
“Wannan kawai shaci-faɗi ne da ake yaɗawa.”
Ya ƙara da cewa: “Babu shakka Jonathan ɗan Najeriya ne kuma yana da damar tsayawa takara idan ya so.
“Amma ba wani abu daga PDP kan wannan magana. Shi ma tsohon shugaban bai nuna sha’awar fitowa takara ba, balle mu ce mun tuntuɓe shi a kan haka.”
Kakakin ya jaddada cewa PDP, tana da ’yan takarar da suka cancanta daga cikin gwamnoni da shugabanni da dama a halin yanzu, kuma jam’iyyar ba ta dogara da mutum ɗaya kawai don neman shugabancin ƙasa.
Duk da haka, wasu suna ganin Jonathan zai iya zama ɗan takarar maslaha saboda rarrabuwar kai da ake samu cikin jam’iyyar.
Sai dai Abdullahi, ya ce PDP ba za ta dogara da wani mutum da bai nuna sha’awar fitowa ba.
Ya kuma ƙara da cewa: “PDP ta kasance jam’iyya mai ƙarfi wacce ba ta sauya aƙida ko sunanta tun da aka kafa ta ba.
“Har yanzu ita ce jam’iyyar da ta fi kowace daɗewa a tarihin siyasar Najeriya.”