✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a soma tiyatar haihuwa kyauta a Najeriya — Ministan Lafiya

Wannan muhimmin mataki ne da zai taimaka wajen rage yawan mace-macen mata a lokacin haihuwa.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa daga yanzu kyauta za a riƙa yi wa mata tiyatar haihuwa, wato Cesarean Sections (C.S) a duk faɗin ƙasar.

Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate ne ya sanar da hakan a yayin wani taron kwanaki biyu na bitar harkokin kiwon lafiya da aka gudanar a Abuja.

Pate ya ce wannan na ɗaya daga cikin matakan da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka domin rage mace-macen mata da ake samu a lokacin haihuwa a faɗin ƙasar.

Haka kuma, Ministan ya ce wannan na ɗaya daga cikin manufofin Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ganin an bai wa mata kulawa ta musamman.

Ministan ya ƙara da cewa, bai dace ba a ce wata mace ta mutu a Najeriya saboda ba ta da halin biyan kuɗin tiyatar haihuwa.

Bayanai na cewa wannan matakin zai taimaka wajen magance wahalhalu, da kashe maƙudan kuɗaɗen da ake fama da su yayin da sauran ababen buƙatar yi wa mace tiyatar ta haihuwa.