Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta ce za a shafe kwana hudu a jere ana tafka ruwan sama a wasu jihohin Arewacin Najeriya guda biyar da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Jihohin da lamarin zai shafa sun hada da wasu sassa na jihar Kaduna da Neja da Filato da Bauchi da Nasarawa da kuma Abuja.
- Kashi 10 na masu shan miyagun kwayoyi a Najeriya – yan Kaduna ne – NDLEA
- Akwai yiwuwar Buhari ya ciyo bashin N11trn don cike gibin kasafin 2023
NiMet ta kuma ce za a sami matsakaicin ruwan sama a jihohin Kwara, Oyo, Kogi, Ogun, Ekiti, Ondo, Sakkwato, Katsina, Zamfara, Kebbi, Kano, Jigawa, Yobe, Borno, Gombe, Adamawa, Taraba, Binuwai, Kuros Riba, Akwa Ibom, Ebonyi, Enugu, Abia, Imo, Anambra, Ribas, Edo da kuma Delta.
Hukumar ta kuma ce za a sami ruwan sama kadan-kadan a ragowar sassan Najeriya.
“A sakamakon ruwan da ake hasashen samu a jihohin Kudanci da Tsakiyar Najeriya na kwanaki biyu a jere, akwai yiwuwar a sami ambaliyar ruwa a kan hanyoyi saboda koguna za su cika su batse.
“Kazalika, za a sami guguwa wacce za ta biyo bayan matsakaicin ruwan saman da za a samu a a dukkan sassan Arewaci da Tsakiyar Najeriya a cikin kwanakin,” inji hukumar.
NiMet ta kuma shawarci jama’a da su guji tuki a cikin ruwa, su share magudanun ruwa sannan kada su tsaya a karkashin bishiya ko ginin da ba shi da kariya kuma su karkashe kayan lantakinsu lokacin ruwan.