Lionel Messi ya sanar da cewa zai yanke shawara kan al’amura da dama dangane da makomarsa bayan kammala gasar cin kofin duniya da kasar Qatar za ta karbi bakunci.
Messi wanda a halin yanzu ba shi da tabbaci a kan makomarsa, ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da manema labarai, jim kadan bayan wasan neman tikitin halartar gasar Cin Kofin Duniya da tawagar Argentina ta lallasa Venezuela da kwallaye 3-0, wanda dan wasan ya ci daya daga ciki.
- Koriya ta Arewa na fuskantar barazana kan gwajin makami mai linzami
- Dimokuradiyyar da babu dimokuradiyya a cikinta
Jaridar wasanni ta Goal ta ruwaito cewa, kwallon da Messi ya ci, ita ce ta 81 a wasanni 158 da ya bugawa tawagar kasar.
Wannan kakar dai ta kasance mai wahala ga Messi bayan da ya gaza haskawa wajen nuna bajinta kamar yadda aka saba gani tun bayan da ya koma kungiyar Paris Saint-Germain daga Barcelona.
A shekarar bara ne dai tauraron dan kwallon na Argentina ya jagoranci kasarsa zuwa nasarar lashe kofin gasar Copa America.
Sai dai, yayin da tsohon dan wasan Barcelona ke ci gaba da samun nasara tare da tawagar kasarsa Argentina, har yanzu bai samu yadda yake so a Faransa ba, inda ya zira kwallaye biyu kacal a gasar Ligue 1, kwallaye biyar kuma a gasar zakarun Turai, yayin da ya gaza taimakawa PSG wajen hana fitar da ita a zagaye na biyu, a gasar cin kofin Zakarun Turai.