✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a sake rufe wuraren ibada a Kaduna —Ma’aikatar Lafiya

Gwamna El-Rufai ya killace kansa a karo na biyu bayan makusantansa sun kamu da COVID-19

Gwamnatin Jihar Kaduna na shirin sake rufe wuraren ibada da kasuwanni a jihar bayan sake bullar COVID-19, wanda ta kai ga killace Gwamna Nasir El-Rufai a karo na biyu.

Kwamishinar Lafiya ta jihar, Amina Mohammed-Baloni, ta ce za a dawo da dokar kulle da hana taruwar jama’a ne domin takaita yaduwar COVID-19 a jihar inda yawan sabbin masu kamuwa da cutar ke ta hauhawa.

“Zuwar ranar Juma’a 11 ga Disamba, 2020 mutum 117 sun kamu da cutar daga cikin mutum 518 da aka yi wa gwaji — mutum daya ke na daga cikin komane mutum hudu da aka yi wa gwaji yana da cutar”, inji Amina Baloni.

A safiyar Asabar ne Gwamna Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya fara killace kansa na tsawon kwana 14, bayan sakamakon gwaji ya nuna wasu daga cikin makusantansa sun kamu da cutar ranar Juma’a.

Kwamishinar Lafiyar Jihar ta ce saboda hadarin COVID-19 ga rayuwa, “idan masu kamuwa suka yi ta da karuwa, abin zai gagari jami’an lafiya da kayan aikinmu, su duk da kokarin da ake yi na inganta bangaren’’.

Gargadin na nufin yiwuwar rufewa da kuma hana zuwa wuraren taruwan jama’a da suka hada da wuraren ibada, kasuwanni, makarantu, ma’aikatu, wuraren motsa jiki da na shakatawa da sauransu.

A jawabinta ga ’yan jarida ranar Asabar, kwamishinar ta ce da ma jihar ta yi tsammanin yiwuwar samun karuwar masu cutar idan aka janye dokar kullen da aka sanya da farko.

Sai dai ta bayyana damuwa game da yawan alkaluman, inda a rana guda (26 ga Nuwamba) kadai karin mutum 74 sun kamu da cutar a jihar.

Hakan a cewarta ya tuno wa jihar da halin da ake cike lokacin ganiyar cutar daga watannin Afrilu zuwa Yuni, 2020.

Saboda haka ta yi kirage iyalai da daidaikun mutane da su yi hattara domin hana bazuwar cutar.

“Muna ba wa daukacin al’umma kwarin gwiwa cewa su ci gaba da kiyaya matakan kariyar cutar kamar yadda hukumomi suka ayyana”, inji Baloni.