✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Za a sake dawo da dokar kulle a Osun’

Gwamatin Jihar Osun ta ce akwai yiwuwar ta dawo da dokar kulle sakamakon kamuwar mutum 22 da cutar a cikin awa 24. Kwamishinan Lafiyan Jihar,…

Gwamatin Jihar Osun ta ce akwai yiwuwar ta dawo da dokar kulle sakamakon kamuwar mutum 22 da cutar a cikin awa 24.

Kwamishinan Lafiyan Jihar, Rafiu Isamotu, ya ce gwamnatin na duba yiwuwar sake rufe jihar sakamakon lamarin da ya faru washegarin ranar da wasu mutum 17 suka kamu.

“Ranar Alhamis mun sanar cewa mutum 17 sun kara kamuwa a jiharmu. Abin takaici kuma mun kara samun mutum 22.

“Idan muka dubi abin da ya faru a baya, wannan babban abin damuwa ne kuma dole mu dauki mataki domin yaki da coronavirus bai kare ba”, inji shi.

Kwamishinan ya ce 11 daga cikin sabbin masu cutar an gano su daga cikin wadanda suka yi hulda da masu cutar ta coronavirus a yankin Ede da ke Osogbo, babban birnin jihar.

Da yake kokawa kan yadda jama’a ke kin bin ka’idojin kariya, kwamishinan ya ce “Kwayar cutar na nan tare da mu. Dole mu bi matakan kariya, idan har muna so mu hana yaduwarta a cikin al’umma.

Ya ce zuwa lokacin, mutum 54 ne ke dauke da cutar daga cikin mutum 106 suka taba kamuwa a jihar, wadanda 47 daga cikinsu sun warke, wasu biyar kuma ta yi ajalinsu.