Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Fatakwal babban birnin Jihar Ribas ta yanke wa wasu mutum biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin daukewa da kuma kisan wani mutum mai suna Mista Anthony Okoro.
Mutanen, Oluchi Charles, Miracle Anumuna, Ifeanyi Simon, Koko Basset da kuma Uchenna Stanley Amaechi dai an zarge su ne da hada baki wajen aikata laifuka guda 10 da suka shafi hadin baki domin aiwatar da sata, fashi da makami, garkuwa da kuma kisan kai.
Kotun ta wanke sauran mutum biyun da ake zargin, Chukwudi Etete da Anthony Ugwu tare da sakin su saboda rashin samun hannunsu a ciki.
- An yankewa matar da ta kashe mijinta hukuncin kisa ta hanyar rataya
- Kungiyar IPOB ta kashe Hausawa Biyu a Ribas
A ranar 26 ga watan Mayun 2016 ne dai aka zarge su da kai hari kan Mista Anthony mazaunin yankin Woji da ke Fatakwal sannan suka harbe shi suka kuma tafi da gawarsa.
Kazalika, an same su da laifin satar motoci kirar Range Rover da kuma Kia, da talbijin, wayar salula da sauran muhimman kaya mallakin mamacin.
Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a George Omereji ya ce masu shigar da karar sun tabbatar da zarge-zargensu kan wadanda aka yanke wa hukuncin, yayin da kuma ya sallami sauran mutum biyun saboda gano cewar ba su da hannu a ciki.
Ya kuma ce shari’ar ta samu wadanda ake zargin da hannu dumu-dumu a kisan Mista Anthony din.