✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a rataye mutumin da ya kashe matarsa da danta a Adamawa

Mijin ya amsa cewa ya sassari matar tasa da Gatari sannan ya daddatsa dan da Adda.

Babbar Kotun Jihar Adamawa ta yanke wa wani mutum mai suna Bangos Adams hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe matarsa da danta.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Fatima Ahmed Tafida ce ta yanke hukuncin inda ta ce ta gamsu da hujjojin da aka gabatar kan zarge-zargen da ake yi masa guda biyu.

An dai zargi Bangos, wanda ya fito daga kauyen Janjaba da ke Karamar Hukumar Gombi ta Jihar Adamawa da zargin kashe matarsa, Regina Bangos da danta, Revelation James.

Aminiya ta gano cewa mijin, wanda manomi ne an zarge shi tun da farko da kashe matar tasa ta hanyar saranta da Gatari a ka, sannan ya daddatsa dan nata da Adda, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsu nan take.

Bangos dai ya shaida wa kotun cewa ya auri matar ne bayan da aurenta ya mutu da tsohon mijinta, inda ya ce ta zo da dan nata ne gidansa a matsayin agola.

Ya ce a duk lokacin da ya sami rashin fahimta da matar, ta kan yi masa barazanar cewa za ta koma gidan tsohon mijin nata, kuma tana samin goyon bayan dan nata.

Bangos ya ce a ranar 15 ga watan Yunin 2021, suna zaune a gida ne sai matar ta bukaci a bata hatsi za ta yi girki, amma sai ya ce mata ta tafi dakin girki ta debo a can.

Sai dai ya ce matar ta ki zuwa dakin girkin, amma ta bukaci ya sayo mata burodi a maimakon haka, amma ya ki inda ita kuma ta fara kunkunai tana barazanar komawa wajen tsohon mijin nata.

Ya ce amsar da ta bashi ce ta fusata shi, sannan ya fara kullatarta da ita da dan nata.

Bangos ya shaida wa kotun cewa bayan sun kwanta bacci ne da daddare ya tashi ya dauko Gatari ya sassara mata a ka.

Mijin ya kuma ce lokacin da matar ta ke fama da radadin saran ne sai ya dauki Adda ya daddatsa dan nata mai shekara bakwai.

Sai dai bayan guduwarsa, daga bisani kungiyar mafarautan yankin sun kama shi tare da damka shi ga hannun ’yan sandan Karamar Hukumar Gombi.