Wata Babbar Kotun Tarayya ta yanke wa wani matashi mai shekara 26 hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe wani manomi.
Lauya mai shigar da kara, Mista Wale Fapohunda ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin, Dele Ojo ya amsa zargin da ake masa na kashe Mista Ajayi Adewole ranar 13 ga watan Satumbar 2018 a garin Iroko-Ekiti da ke Karamar Hukumar Ijero ta Jihar Ekiti.
Wani aminin mamacin da ya bayar da shaida a kotun da ke zamanta a birnin Ado-Ekiti, ya ce Dele ya jima yana satar doya a gonar Ajayi, kafin dubunsa ta cika a ranar da suka yi masa kwanton bauna suka cafke shi da misalin karfe biyun dare.
Shaidan ya ce sun hangi barawon sanye da fitila a goshinsa yana nuna kamar farauta yake yi, alhali kuwa ya fake da farautar ne ya dukufa hako doya a gonar mamacin.
Ya kara da cewa ko da manomin ya shaida barawon tare da kwalla ihu yana kiran sunansa, nan take ya harbe shi ya kuma cika wandonsa da iska.
Daga nan ne kuma inji shi aka garzaya da Mista Ajayi zuwa Asibitin Kwararru na Ijero Ekiti inda aka tabbatar ya rasu.
Da yake yanke masa hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a Abiodun Adesodun ya ce yanayin laifin da aka aikata ba ya bukatar jiran amincewar gwamnan jihar kafin a zartar da hukuncin.
Kafin a kai ga hukuncin dai sai da aka gabatar da mutane hudu a matsayin shaidu a gaban kotun, sai kuma hotunan mamacin, bindigar da aka yi kisan da ita, doya guda biyar da kuma takardar da ke dauke da bayanan amsa laifin wanda ake zargin.