✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 5 sun rasu sakamakon rikicin manoma da makiyaya a Neja

Ana zargin makiyaya da kashe manomin kwana guda bayan ya yi ƙorafi a kansu.

Rikici ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a garin Beji da ke ƙaramar hukumar Bosso a Jihar Neja, inda ake zargin mutum biyar sun rasa rayukansu, ciki har da wasu ’yan gida ɗaya mutum uku.

Rikicin ya faro ne a ranar Litinin, bayan an tsinci gawar wani manomi a gonarsa, kwana guda bayan ya yi ƙorafi kan yadda makiyaya da suka barin shanunsu suna ɓarna a gonarsa.

Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa samun gawar manomin a ranar Talata ya tayar da ƙura, lamarin da ya haifar da zaman ɗar-ɗar a garin Beji da kewaye, musamman da kasuwar mako-mako ta Beji wadda ke ci a ranar Laraba.

Aliyu Mohammed, wani mazaunin garin, ya ce wannan lamari ya jefa jama’a cikin tsananin tsoro da firgici.

“Rikicin ya fara ne bayan an tsinci gawar wani manomi na Gbagi a gonarsa. Ana zargin makiyaya ne suka kashe shi bayan ya yi ƙorafi game da yadda suke lalata gonarsa.

“Akwai tsananin damuwa. A wani lamari makamancin wannan a watan Nuwamban 2023, mutum shida sun rasa rayukansu a ranar kasuwa, wanda hakan ya sa mutanen gari shiga rikicin.

“Muna fatan hukumomi za su ɗauki mataki cikin gaggawa don hana rikicin ya ƙara tabarbarewa a wannan karon,” in ji shi.

Wani Bafulatani ya ce ’yan banga sun tare hanyar Minna-Zungeru, suna sauke Fulani daga motocinsu ta ƙarfi, wanda hakan ya ƙara tayar da hankali.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce zai yi ƙarin bayani bayan ya tattara cikakken bayanai.