✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a rantsar da Joe Biden a matsayin Shugaban Amurka cikin tsauraran matakan tsaro

Za a rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban Amurka na 46 a ranar Laraba, bayan ya lashe zaben shugaban kasar

Za a rantsar da Joe Biden a matsayin Shugaban Kasar Amurka na 46 a ranar Laraba, bayan ya lashe zaben kasar da Shuagaba mai barin gado Donald Trump ya jima yana zargin an tafka magudi a cikinsa.

Za a fara bikin rantsar da Biden ne tare da Mataimakiyarsa, Kamala Harris da karfe 10:30 na safe, misalin karfe 3:30 na yamma kenan a agogon Najeriya.

Dubun dubatar mutane ne ake sa ran za su halarci bikin, ko da yake an takaita yawan mahalartarsa saboda takaita yaduwar annobar COVID-19, wacce ya zuwa yanzu ta hallaka sama da 400,000 a Amurka.

Bugu da kari, an tsaurara matakan tsaro bayan da masu tarzomar goyon bayan Trump sun kutsa kai cikin ginin Majalisar Dokokin kasar wato Capitol a farkon wannan watan.

Fiye da jami’an tsaro 25,000 ne aka girke a sassa daban-daban na birnin Washington DC saboda bikin rantsuwar.

Sai dai Shugaba Trump ya ce ba zai halarci bikin ba, duk da cewa bisa al’ada dukkannin shugabannin kasar da ke raye za su kasance a wurin.

Amma Mataimakin Shugaba Trump, Mike Pence ya ce shi zai kasance a wurin.

Tuni dai Trump ya bar fadar White House inda ya fara shirin gudanar da wani kwarya-kwaryar biki a wani sansanin sojoji da ke kusa da fadar, kafin daga bisani ya wuce zuwa Jihar Florida, inda ake sa ran zai ci gaba da zama a masaukin sa na Mar-a-Lago.

Wani malamin addini na Jesuit, Leo O’Donovan ne dai ake sa ran zai bude taron, sannan shahararriyar mawakiya Lady Gaga za ta rera taken kasar.

Sauran fitattun mutanen da za su halarci bikin sun hada har da fitacciyar mawakiya Jennifer Lopez.

Biden zai gabatar da jawabinsa na farko a al’adance ne bayan rantsuwar wanda shi ne zai zama fitilar da za ta haska alkiblar da gwamnatinsa za ta fuskanta a cikin shekaru hudu masu zuwa.

%d bloggers like this: