✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a raba wa mata tallafin N20,000 —Sadiya Faruq

Buhari na so mata su ja jarin da zai taimaka su yaki talauci.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta raba wa mata tallafin Naira 20,000 domin su ja jarin sana’ar da za su yaki talauci da ita.

Hakan na kunshe ne cikin wani sako da Ministar Agaji da Kula da Ayyukan Jinkai, Sadiya Farouq ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Talata.

Ministar ta ce wannan kudi na tallafi wanda ba bashi ba ne, za a bayar da shi sau daya ne ga matan da ke fama da fatara a kauyuka, da kuma garuwan da ke kusa da birane.

Kudin tallafin za a raba shi ne a dukkannin jihohi 36 na kasar nan, da kuma babban birnin tarayya, Abuja.

Sadiya ta ce wannan kudi za a raba su ne a karkashin wani tsari na Shugaba Buhari da ake yi wa lakabi da mu hada hannu mu tafi tare.

A karkashin shirin, za a ba mata kaso 70, maza kuma kaso 30 na jimillar wadanda za a raba wa tallafin.

An kuma ware kashi 15 na wannan adadi ga masu bukata ta musamman, da wadanda suka manyanta, da ‘yan gudun hijira, da wadanda suka dawo garuruwansu na asali, da marayu, da kuma iyayen marayun.

Ministar ta kuma kara da cewa, ma’aikatarta za ta yi aiki da sauran takwarorinta, da hukumomin da abin ya shafa, da gwamnatocin jihohi, da kungiyoin sa kai, da kuma sauran masu ruwa da tsaki wajen aiwatar da shirin.

Ta ce hakan zai taimaka wajen zakulo wadanda za su ci moriyar tallafin.

Kazalika, ta ce burin shirin shi ne ceto wadanda ke fama da matsananciyar fatara da shugaba Buhari ya kirkiro tun a shekarar 2020.

Gwamnatin Buhari ta sha nanata kudirinta na tsamo ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10.