Gwamnatin Tarayya za ta raba wa namoma bashi mara ruwa na Naira biliyan 600 a yunkurinta na wadata kasa da abinci.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya sanar cewa manoma miliyan 2.4 ne za su amfana da rancen tallafin a fadin Najeriya karkashin shirin bunkasa samar da amfanin gona (APPEALS).
- Najeriya A Yau: Taskun da ’yan gudun hijira ke ciki a Najeriya
- Mutumin da ya fi kowa tsayin hanci a duniya
Ya ba da sanarwar ce a taron bikin baje kolin kayan goma da aka shirya domin bikin Ranar Abinci ta Duniya ta shekarar 2021 a Abuja.
Buhari ya yi bayanin ne ta bakin Ministan Noma da Raya Karkara, Mohammed Abubakar, wanda ya wakilce shi a taron wanda ya gudana a ranar Laraba.
Taken taron na bana shi ne “Ayyukanmu su ne rayuwarmu ta gaba: Samar da wadataccen abinci, Karin lafiyayyen abinci, muhalli da kuma rayuwa mai inganci”.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Noma, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce gwamnatin Buhari ta jima tana bullo da manufofi da tsare-tsare domin samar da wadaccen abinci a Najeriya.