Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya nada tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Gombe, Ahmad Abubakar Walama, a matsayin Sarkin Malaman Gombe.
Kafin nadin nasa, Ahmad Walama, ya taba zama Shugaban Karamar hukumar Dukku daga shekara ta 2004 zuwa 2011, sannan ya zama Kwamishinan a shekarar 2011 zuwa 2019.
- Mai ’ya’ya 8 ta sake haifar ’yan 3 a Kebbi
- Za mu duba kudurin da zai ba Sarakuna aikin yi a gwamnatance — Abbas
Da yake gabatar da sakon Sarkin ga Sabon Sarkin Malaman, Shamakin Gombe, Alhaji Usman Muhammad, ya ce sun kawo wa Sarkin Malaman sakon domin su sanar masa cewa an ba shi sarautar gidansu wanda mahaifinsa, marigayi Alkali Bappah ya rike kafin rasuwarsa.
Shamakin ya ce Sarkin ya ba shi sarautar ce bisa cancantarsa da kuma dacewa na ya gaji mahaifin nasa.
Da yake zantawa da manema labarai bayan taron murnar da ya shirya a gidan mahaifinsu Ahmed Walama, ya ce wannan rana ce ta farin ciki a gare shi domin irin ta sau daya take zuwa a rayuwa.
A cewar sa Sarkin Malamai jakadan Sarki ne a tsakanin al’umma wanda kuma zai yi kokari ya sadar da jakadanci na gari a tsakaninsa da malaman Jihar Gombe.
Daga nan ya gode wa Sarkin bisa ganin dacewarsa ya ba shi wannan sarauta duk da cewar ’yan uwansa da dama da su ma suka cancanta.