Gwamnatin Tarayya na shirin mayar da Lambar Shaidar Dan Kasa ta NIN ta maye gurbin Lambar Tantance Shaidar Ajiyar Banki ta BVN.
Da yake sanar da haka, Ministan Sadarwa, ISa Ali Pantami ya ce nan gaban Lambar NIN za ta maye gurbin BVN da sauran bayanan ’yan Najeriya da sauran hukumomi suka tattara.
- An cafke mutane 3 masu dillacin makamai a Kebbi
- Kwamandan ’yan bindiga Daudawa ya mika wuya a Zamfara
- An kama tsohon Shugaban Karamar Hukumar ‘mai taimakon’ ’yan bindiga
- Kyanwa ta rayu ba abinci tsawon mako uku
Pantami ya ce, “Na yi wa Kwamitin Dore Cigaban Tattalin Arziki na Kasa jawabi inda na ja hankalin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) cewa muna bukatar musanya BVN da NIN saboda BVN tsari ne na da Bankin ya yi bankuna; NIN kuma dokar kasa ce, kuma a ko’ina dokar kasa na gaba da tsarin da wata hukumar gwamnati ta yi”, inji ministan.
Da yake ran gadin yadda ake gudanar da rajistar NIN a ranar Litinin, Pantami ya ce Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) ce ke da alhakin tara bayanan ’yan Najeriya da sauran hukumomi zu su dogara da su wurin samun bayanai.
“A Majalisar Daraktocin NIMC akwai Gwamnan CBN, Darakta-Janar na DSS, Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS), Shugaban INEC, Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro (NSA), Hukumar Kidaya ta Kasa da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya.
“Wannan ke nuna cewa rumbun bayanan NIMC shi ne tushe da kowace hukumar gwamnati za ta yi amfani da shi domin kare bayanai, kuma a yanzu mu ne kan gaba a Afirka” inji Pantami.
Ya ce a halin yanzzu rumbun tara bayanan NIMC na da aminci kashi 99.9%, wanda shi ne mafi kololuwar mataki a duniya domin babu inda ake da kashi 100%.
“Mun yi kokarin tabbatar da cikakken aminci ba tare da barin an yi kutse ko cin ha’inci ba a aikin da aka ba mu ba,” inji shi.