Gwamnatin Kano ta yi wa masu cutar AIDS 533 rajista domin ba su kulawa daga dukkacin cututtuka kyauta a cibiyoyin lafiyarta da ke Jihar.
Shugabar Hukumar Kula da Lafiya ta Hadin Gwiwa ta Jihar Kano, (KSCHMCA) Dokta Halima Muhammad Mijinyawa ce ta sanar da haka ranar Litinin.
- Sojoji ne suka ceto Daliban Kankara —Fadar Shugaban Kasa
- Saudiyya ta hana ’yan kasashen waje zuwa Umrah
- Mutumin da ya kera kofar Dakin Ka’aba ya rasu
- Abin da ya sa Aisha Buhari ta yi batar dabo
“Hakan da daga cikin kasonsu na shigar da su cikin asusun kula da lafiya na bai-daya a jihar,” inji ta.
Ta ce asusun dauki ne daga Gwamnatin Tarayya na adashin gatan kula da lafiya wanda zai rika kulawa da kyauta da lafiyar mata, kananan yara, tsofaffi da nakasassu da sauransu.
Tun da farko, Darakta-Janar na Hukumar Yaki da Cutar Aids ta Jihar Kano (KSACA), Dokta Sabitu Shu’aibu Shanono, ya ce shigar da masu cutar tsarin ya ba da damar koyi da Gwamnati na sa su a cikin tsarin NHIS na inshorar lafiyata ta kasa.