✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a koya wa tubabbun ’yan Kalare 20 Sana’a

Wata kungiya mai zaman Kanta mai suna Trive Trek Enterprises Centre da hadin gwiwar Rundunar ’Yan Sandan Gombe da tallafin gwamnatin jihar za su koya…

Wata kungiya mai zaman Kanta mai suna Trive Trek Enterprises Centre da hadin gwiwar Rundunar ’Yan Sandan Gombe da tallafin gwamnatin jihar za su koya wa tubabbun matasa ’yan Kalare sana’oin dogaro da kai. 

Shugaban cibiyar, Aliyu Babangida (National), ya ce cibiyar wacce ta ƙunshi kamfanoni bakwai, ta gamsu da yadda matasan suka himmatu kan tafarkin zaman lafiya, don haka ta yanke shawarar horar da su sana’o’in dogaro da kai don a samu dorewar zaman lafiya da tabbatar da cewa basu koma ga tsohuwar sana’ar su ta kalare ba.

Aliyu yace fannonin da za su horar da matasan sun haɗa da yadda ake aikin wayarin din lantarki da yadda ake dasa na’urorin samar da wuta daga hasken rana da dasa kyamarar tsaro ta CCTV da dai sauransu.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Hayatu Usman ya ce rundunar ta bullo da shirin ne a yunkurinta na magance rashin tsaro da yawan matasa marasa aikin yi a jihar.

Ya ce a wannan karon, shirin zai koyar da matasa 20 ne daga cikin ’yan Kalare 200 da suka tuba bayan sun addabi jihar da ayyukan dabanci a baya.

Hayatu Usman ya ce a baya rundunar ta kama matasan da ke addabar yankin da dama, ta gurfanar da su, inda kotu ta daure su a kurkuku.

Ya ce, amma abin mamakin shi ne idan suka fito daga gidan kaso, maimakon su canza hali, dorawa suke daga inda suka tsaya.

CP Hayatu ya ce amma wannan sabon matakin na koyar da sana’a ga ’yan dabar ya fara haifar da kyakkyawan sakamako a jihar, domin fiye da ’yan kalare 250 ne suka watsar da makamansu suka rungumi zaman lafiya.

Ya yaba wa cibiyar ta Thrive Trek bisa goyon bayan wannan yunkuri, sannan ya bada tabbacin cikakken goyon bayan rundunar don cimma manufofin da aka sanya a gaba.

Kwamishinan ya yi kira ga sauran kungiyoyi da mawadata da cewa su shigo su dafa wa wannan yunƙuri wajen karfafa musu guiwa, domin ganin Jihar Gombe ta samu zaman lafiya da ci gaba.

Da yake tsolaci mai bai wa gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin tsaro AIG Zubairu Mu’azu (mai murabus), cewa ya ce gwamnatin jihar tana yin iya kokarinta ta wurin tallafa wa matasa ta hanyar koya musu sana’o’i da ba su ayyuka daban-daban kamar aikin samar da tsaro da kula da zirga-zirgar ababen hawa da alkinta muhalli na GOSTEC, da kuma kafa makarantar horar da matasa da ke garin Boltongo.

AIG Mu,’azu ya ce yanzu haka an kammala kashi 90 cikin 100 na gina makarantar horar da matasa fiye da 200 sana’o’i daban-daban a lokaci guda, yana mai cewa idan ta kammala, makarantar za ta zama babbar cibiyar horar da tubabbun ’yan Kalare.

Matasan da suka fito daga unguwanni daban-daban na cikin garin Gombe, sun yabawa rundunar ’yan sanda da cibiyar da kuma gwamnatin jihar bisa wannan yunkurin na sauya musu rayuwa.

Sun kuma ba da tabbacin cewa za su ba da himma kan sabin sana’o’in da za a koya musu.