✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Duk wanda ya shiga Kaduna za a killace shi’

Gwamnatin Kaduna ta gargadi matafiya masu shirin shiga jihar su kiyaye ko kuma su fada yanayin da za a killace su har tsawon kwanaki 14…

Gwamnatin Kaduna ta gargadi matafiya masu shirin shiga jihar su kiyaye ko kuma su fada yanayin da za a killace su har tsawon kwanaki 14 a inda aka tanadar ko kuma su koma inda suka fito.

An fitar da sanarwar ne bayan da gwamnatin jihar ta yi kwamitin yaki da yaduwar annobar Covid-19, wannan dokar za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis 9 ga Afrilu 2020.

Gwamnatin jihar ta ce za a rufe duk wasu hanyoyin shiga jihar har sai dai wadanda aka amince su wuce. Matafiyan da aka dakatar kuwa sai dai su koma inda suka fito, wadanda kuwa aka bari suka shiga za a killace su har zuwa kwanaki 14 a cibiyar killace mutane, da aka tanadar don masu dauke da Coronavirus.

An shawarci duk wanda bai da tabbatarcen katin shaida ya soke tafiyarsa na shiga jihar Kaduna.

Jami’an tsaro za su umarci duk wanda ba a amince ya shiga jihar ba da ya koma inda ya fito, kamar hanyoyin da suka hada da: Kaduna zuwa Abuja da hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da hanyar Kaduna zuwa Zariya, sai Zariya zuwa Kano da hanyar Bwari zuwa da Jere zuwa Kagarko, da hanyar Gumel zuwa Kwoi sai zuwa Keffi, da hanyar Zariya zuwa Funtua da kuma hanyar Jos zuwa Manchock.

Wannan dokar ta shafi wasu hanyoyin shiga da fita da ke cikin jihar da ba a bayyana su ba cikin sanarwar.

Jihar ta tanadar wajen killace mutane don kare lafiyar su daga cutar COVID -19